IQNA

‘Yan Ta’adda 11 Sun Halaka A Kasar Mali

13:28 - July 23, 2018
Lambar Labari: 3482843
Bangaren kasa da kasa, ‘yan ta’adda 11 ne suka halaka a kasar Mali sakamakon dauki ba dadin da aka yi tsakanins da jami’an soji.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ma’aikatar saron kasar Mali ta sanar da cewa, ‘yan ta’adda 11 ne suka halaka a kasar biyo bayan wani dauki ba dadin da aka yi tsakaninsu da jami’an sojojin kasar.

Bayanin ya ce ‘yan ta’addan sun danawa jami’an tsron kasa wani tarko ne a lokacin da suke yin sintiri, inda suka samu damar kasha soja guda da kuma jikkata wasu.

Sai a nasu bangaren jami’an sojin kasar ta Mali sun mayar da martani mai karfi, inda suka kashe ‘yan ta’adda goma sha daya tare da jikkata wasu.

Ko ranar Juma’a da ta gabata an yi wani dauki ba dadi a kan iyakokin kasashen Mali da kuma Nijar, inda aka akashe ‘yan ta’adda kimanin ashirin tare da jikkata wasu da dama.

3732451

 

 

 

 

 

 

captcha