IQNA

An Gudanar Da Taro Mai Taken Taron Matasa Musulmi A Ghana

23:57 - September 05, 2018
Lambar Labari: 3482956
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taron na shekara-shekara namatasa musulmi ‘yan Ahmadiyyah a Ghana.

 Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, masu bin aidar Ahmadiyya ne suka shirya wannan zaman taro, wanda ya samu halartar mutane sama da dubu uku daga ciki da wajen kasar Ghana.

Daga cikin kasashen da suka halarci taron akwai Najeriya, sai kuma Burkina Faso, da Mali da kuma kasar Uganda gami da Ivory Coast.

Wanna shi ne karo na talatin da tara da kungiyar Ahmadiyya take shirya taron matasanta na shekara-shekara a kasar ta Ghana, inda akan gabatar da jawabai kan lamurra da suka shafi addini da kuma rayuwar matasa.

Alhaji Maulawi Nur Muhammad Bin Saleh shi ne shugaban Ahmadiyya na yanzu a kasar Ghana, shi ne kuma wanda ya gabatar da jawabia  wurin, dangane da ayyukan da suka sanya a gaba a halin yanzu musamman kan lamarin matasa.

3744248

 

 

captcha