Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na yanar gizo na Rafha cewa, ma’ikatar yada labarai ta kasar Saudiyya ta bayyana kira’ar da aka farwa sanyawa agidan radiyon kur’ani na kasar da cewa ita ce mafi jimawa.
Wannan kira’a an yi ta ne tun shekaru 48 da suka gabata, kuma sheikh Abdullah Khayyat ne ya yi karatun a lokacin a wannan gidan radiyo.
Marigayi Sheikh Abdullah Khayyat ya yi wannan karatu daga aya ta 203 zuwa ta 208 a cikin surat Baqara a shekara ta 1970, kuma har yanzu ana ci gaba da adana wannan sauti.