IQNA

An bude taron kungiyar kasashen larabawa a kasar Tunisiya

23:52 - March 31, 2019
Lambar Labari: 3483508
Taron wanda shi ne karo na 30 a tarihin kafuwar kungiyar, ya sami halartar sarakuna, shugabanni da manyan jami’an gwamnatocin kasashen larabawa.

Daga cikin muhimman batutuwan da taron ya mayar da hankali akansu da akwai na Palasdinu da kuma tabbatar da cewa tuddan Golan mallakin Syria ne ba haramtacciyar Kasar Isra’ila ba.

Sarkin Saudiyya wanda ya halarci taron ya bayyana matsayar kasarsa na kin amincewa da furucin da Amurka ta yi na cewa tuddan Golan yana karkashin HKI.

Shi kuwa shugaban kasar Tunisiya Qa’id Sibsy ya bayyana cewa; Da akwai bukatar taron na kasashen larabawa da ya tabbatarwa da duniya muhimmancin kafa gwamnatin Palasdinu, domin samun zaman lafiya mai dorewa a cikin wannan yankin.

Bugu da kari shugaban na kasar Tunisiya ya ce; Ko kadan bai dace ba a bar yankin larabawa yana ci gaba da zama a matsayin cibiyar rikice-rikice da ayyukan ta’addanci, sannan kuma ya jaddada wajabcin kawo karshen rikicin da kasar Libya take fama da shi.

Bayanin bayan taron zai mayar da hankali ne akan tabbatar da muhimmancin batun Palasdinu da kuma jaddada cewa tuddan Golan mallakin kasar Syria ne.

3800505

 

 

 

 

 

captcha