IQNA

0:00 - May 17, 2019
Lambar Labari: 3483647
Bangaren kasa da kasa, jiragen yakin masarautar Saudiyya sun kashe kananan yara 6 a hare-hare da suka kaddamar kan gidajen jama'a a birnin San'a .

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, jiragen yakin masarautar Saudiyya sun kashe kananan yara 6 a birnin San'a na Yemen.

Wannan na zuwa ne a wasu munanan hare-hare dajiragen yakin na gwamnatin kasar ta Saudiyya suka kaddamar  kan gidajen jama'a fararen hula a wata unguwa da ke cikin birnin San'a fadar mulkin kasar ta Yemen.

Majiyoyin asibiti sun tababtar da cewa, akwai mutane da dama da suka samu raunuka da suke cikin mawuyacin hali, wanda hakan ka iya kara adadin mutanen da suka rasa rayukansu a wadannan hare-hare.

Shekaru fiye da 4 kenan Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa suke kaddamar da hare-hare  akan al'ummar kasar Yemen da sunan yaki da kungiyar Alhuthi, inda suke samun cikakken goyon baya daga kasashen da suke sayar musu da makaman da suke kai hare-jharen da su , musamman Amurka da Birtaniya da kuam Faransa, wanada suke yin cinikin makamai na daruruwan biliyoyin daloli daga kasar gwamnatin Saudiyya a kowace shekara.

3812144

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، yemen ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: