Kamfanin dillancin labaran iqna, Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto cewa, tashar Almasirah ta kasar Yemen ta bayar da rahoton cewa, dakarun Ansarullah sun harba makamai masu linzami ta hanyar jirage marassa matuki a kan filin sauka da tashin jiragen yakin saudiyya a Jizan da ke kusa da iyaka da kasar Yemen.
Rahoton ya ce hare-haren na zuwa a wani mataki na daukar fansa kan kisan mata da kanan yara da rusa masallatai da makarantu da cibiyoyin ilimi da na kiwon lafiya da Saudiyya da ‘yan korenta suke yi a kasar Yemen ne, inda a cikin wannan makon hare-haren saudiyya sun yi sanadiyyar mutuwar mata da kananan yara a yankuna daban-daban a cikin gundumomin Hajja, Ta’iz da kuma San’a.
A cikin makon da ya gabata ba mayakan na Ansarullah sun harba makamai masu linzamiakan daya daga cikin manyan matatun mai na kasar Saudiyya harin da ya yi babbar barna, duk kuwa da cewa daga bisani mahukuntan na Saudiyya sun da’awar cewa an harba makaman kan biranan Makka da Jiddah ne, ba tare da nuna wata hujja ko alama da za ta iya tabbatar da hakan ba.