IQNA

Jagora Ya Ce Da Matasan Faransa:

Ku Tambayi Shugaban Kasarku Me Yasa Yake Goyon Bayan Cin Zarafin Ma’aiki ?

22:05 - October 29, 2020
1
Lambar Labari: 3485317
Tehran (IQNA) Jagoran Iran ya aike da sako zuwa ga matasan Faransa, dangane da cin zarafin manzon Allah (SAW) a kasar.

Jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya aike da wani sako zuwa ga matasan kasar Faransa, dangane da abin da yake faruwa na cin zarafin manzon Allah (SAW) a kasar.

A cikin sakon nasa wanda aka wallafa a shafinsa na twitter, jagora ya ce da matasan kasar Faransa; ku tambayi shugaban kasarku kan cewa, me yasa yin batunci ga manzon Allah ya zama ‘yanci ne a kasar Faransa?

Shin ma’anar ‘yanci ita ce yin batunci da tozarci, musamman ga mutane masu daraja? Shin wannan aikin wawanci bai zama tozarta musulmi da suka kada masa kuri’a ba har ya zama shugaban kasa?

Tambaya ta biyu kuma ita ce; shin me yasa yin shakku kan batun kisan yahudawa a yakin duniya na biyu ya zama laifi, idan ma har wani ya nuna shakku kan faruwar haka a kasar Faransa, to za a daure shi ne a gidan kaso, amma kuma yin batunci da toarci ga manzon Allah (SAW) ya zama ba laifi ba ne, kowa yana da ‘yancin yin hakan?

 

3931922

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Hafiz kiyawa
0
0
Allah ya daukaka musulinci
captcha