IQNA

An Yi Wa Jagoran Juyi Na Iran Allurar Rigakafin Corona Wanda Masana Na Kasar Ta Iran Suka Ta Yi

23:44 - June 25, 2021
Lambar Labari: 3486047
Tehran (IQNA) a yau Juma'a an yi wa jagoran juyin juya halin muslunci na Iran allurar rigakafin cutar corona da Iran din ta samar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a yau Juma'a an yi wa jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei allurar rigakafin cutar corona da masana na Iran din suka samar.

Jagoran ya ce dama yana jiran Iran ta samar da nata rigakafin ne domin a yi masa wanda aka samar a gida, kuma a cikin ikon Allah da taimakonsa, masana na kasar Iran sun iya samar da wannan rigakafi cikin nasara.

Ya ce tun farko ba ya da sha'awar a yi masa rigakafin cutar corona wanda kasashen ketare suka samar, domin kuwa yana son ya yi alfahari da himma da kokari irin na masanan kasarsa, saboda haka ne ya jira har sai da aka kammala hada rigakafin da Iran ta samar.

Haka nan kuma jagoran ya kara da cewa, babu laifi idan mutane sun yi amfani da rigakafin da aka samar a wajen kasar, kuma za a iya hada biyu na waje da na cikin gida duk a yi amfani da su matkar an samu tabbaci a kan wanda aka shigo da shi.

 

3979919

 

captcha