IQNA

An Tarjama Wasu Hudubobin Littafin Nahjul Balagha Na Imam Ali (AS) A Cikin Harshen Swahili

16:45 - September 07, 2021
Lambar Labari: 3486280
Tehran (IQNA) an tarjama wasu wasu daga cikin hudubobin littafin Nahjul Balagha na Imam Ali (AS) a cikin harshen Swahili.

Cibiyar kula da harkokin aladun muslunci a kasar Tanzania ta sanar da cewa, an tarjama hudubobin littafin Nahjul Balagha na Imam Ali (AS) a cikin harshen Swahili.

Cibiyar ta sanar da cewa, an tarjama hudubobin da suke yin magana a kan kare hakkokin bil adama da kuma hakkokin mata a mahanga ta addini.

Wannan tarjama an mayar da ita ta zama littafi mai zaman kansa, wanda a halin yanzu an buga kwafi 1000 na littafin, kuma za a ci gaba da buga shi domin amfanin mutane.

 

 

3995777

 

 

captcha