IQNA

Karfafa Hanyoyin Koyar da Kur’ani A Aljeriya

23:03 - May 22, 2017
Lambar Labari: 3481540
Bangaren kasa da kasa, an gabatar da shawarwari dangane da muhimmancin gudanar da gyara abangaren koyar da kr’ani a Alljeriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na Al-shuruq cewa, Babban sakataren cibiyar kula da harkokin kur’ani ta kasar Aljeriya da ke karkashin ma’aikatar addinai ta kasar ya bayyana cewa, tsarin koyar da kur’ani a yankunan karkara na bukar gyare-gyare.

Ya bayyana hakan ne a wurin taron da aka gudanar a jahar Girdaya, taron dai ya shafi ayykan koyar da kur’ani a makarantun gargajiya ne, wadanda suke yin amfani da alluna wajen karatu tsarin da ake bi tun daruruwan shekaru da suka gabata akasar.

Dangane da irin tsarin da ya kamata abi wajen koyarwar, ya bayyana cewa malaman suna bukatar wasu taruka na horo na musamman, inda za su koyi wasu hanyoyi na zamani ta yadda yaro zai iya gama karatu a cikin wani kayyadadden lokaci, maimakon ya yi ta karatu bai san ranar gamawa ba.

Baya ga haka kuma daliban da suke makamarantun allo suna da kokari matuka suna gane karatu a mafi yawan lokuta fiye da wasu da ke yin karatun a makarantu na zamani, saboda haka za a rika basu damar wucewa gaba domin kara fadada karatunsu har zuwa makarantu na gaba.

3601638


captcha