IQNA

Sabon Bincike Kan Harshen Karatun Kur’ani

23:34 - January 26, 2018
Lambar Labari: 3482336
Bangaren kasa da kasa, Said Bukhait Mubarak wani masani ne mai bincike kan kur’ani mai tsarki, wanda ya fara gudanar da wani sabon bincike kan harshen kur’ani.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar kasar Oman ta Alwatan cewa, Said Bukhait Mubarak wani masani ne dan kasar Oman mai bincike kan kur’ani mai tsarki wanda ya fara gudanar da wani sabon bincike a halin yanzu kan harshen kur’ani ta fuskar tabbatarwa da kuma sharewa.

Bayanin ya ce wannan masani yana gudanar da bicikensa bisa harshen larabaci wanda ake karanta kur’ani da shi, musamman ganin cewa dukkanin kiraoi bakwai da ake da su suna a matsayin abin da mafi yawan musulmi suke la’akari da shi.

Haka nan kuma wasu daga cikin kiraoin suna karanta wasu kalmomi mabanbanta tsakaninsu da sauran wanda dukkan hakan yana bukatar gudanar da bincike ta sabuwar hanya.

Malam kur’ani dai sun tafi a kan cewa wadannan kiraoi ana gina su ne kan labari mafi inganta wanda ya zo daga sahabbai da kuma tabi’ai, amma babu wanda zai ce nasa ne dai kawai.

Kiara’a da aka fi amfani da ita  aduniya  halin yanzu dai ita ta hafs, kuma da dama daga cikin kasashen musulmi suna yin amfani da a matsayin kira’ar kur’ani da aka aminta da ita.

Ya ce binciken nasa ba zai takaitu da wannan kira’a ba kawai, domin sauran ma ya kamata a yi bincike a kansu kuma a san irin dalilin da suka dogara da su.

3685456

 

captcha